Labarai
Shugaban Amurka Ya Janye Daga Takara Bayan ‘Yan Ƙasar Sun Nuna Ganawarsa
Shugaban Amurka Ya Janye Daga Takara Bayan ‘Yan Ƙasar Sun Nuna Ganawarsa
Shugaban Ƙasar Amurka Joe Biden ya janye daga takara a zaben ranar 5 ga watan Nuwamba, bayan da al’ummar kasar suka nuna rashin dacewar tsaywarsa takara a karo na biyu.
A wani rubutu da ya wallafa a shafin X, a yau Lahadi, shugaba ya ce zai ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban kasa da kuma babban kwamandan rundunar har sai wa’adin sa ya kare a watan Janairu 2025.
Joe Biden ya kuma yi nuni da mataimakiyarsa Kamala Haris, a matsayin zaɓinsa da ya ke so ta maye gurbinsa ta yi wa jam’iyyarsu ta Democrat takara.