Shugaban Ƙasa Tinubu ya Chancanci Yabo kan ƙoƙarin
TSARO A NAJERIYA: Shugaban Ƙasa Tinubu ya Chancanci Yabo kan ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar ta’aàddañci a Arewacin Nageriya:
Misali, hanyar Abuja zuwa Kaduna a baya kafin zuwan Shugaba Tinubu kusan kullum sai an sace mutane matafiya masu zuwa Jihohin Arewa maso Yamma wanda kowa ya san wannan Jihohin sune Arewa su ne Nageriya amma yanzu shiru babu masu satar mutane, matafiya sun rage tsoro da shakkun bin Hanyar a yanzu. Wannan Abin a yaba masa ne.
Bayan haka, duk wasu manya-manyan jiga-jigan jigon ta’âddañci a Arewacin Najeriya yanzu haka yawancin su suna hannu.
Kǎshè-kâshèn al’umma da ƴan ta’âdda ke yi yayi sauƙi domin ko mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu ya bayyana cewa adadin mǎce-macên da ke da alaƙa da ta’ãddañci a Najeriya ya ragu sosai daga 2,600 a kowane wata zuwa ƙasa da 200 a yanzu.
Mista Ribaɗu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a wajen taron yaƙi da ta’âddañci na ƙasashen Afirka da aka fara a ranar Litinin da ta gabata.
Muna murna da wannan nasara da ake samu kan sha’anin tsarô a Najeriya.