E News

Shugaba Tinubu Ya Bukaci Yan Kasa Suyi Addu’a

RAMADAN: Shugaban Kasa Bola Ahmad TINUBU YA Bukaci Yan Kasa Najeria Da Su Yiwa Ƙasa Addu’a

Majiyar mu ta ruwaito shugaba Tinubu na bayyana wannan buƙata yau a masallacin fadar shugaban ƙasa, a lokacin da ya bi sahun al’ummar musulmai wajen buɗe fara Tafsirin Alqur’ani mai girma a bana.

Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan ƙasar da su himmatu wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da wadata, sannan kuma su nunawa juna ƴan’uwantakar musulunci ta hanyar taimakekeniya ga juna da tallafawa masu ƙaramin ƙarfi.

Shugaba Tinubu ya kuma ƙara da bayyana godiya ga Allah da ya nuna mana zagayowar watan Ramadan. Da gode masa bisa ni’imar lashe zaɓe da kasancewarsu ƴan Najeriya.

“Tabbas abubuwa sun yi tsanani, amma Allah ya umarce mu da mu kasance masu sadaukarwa, da horar da kawunanmu, da tallafawa mabuƙata sannan mu kasance mutanen kirki”. -Shugaba Tinubu.

Shugaba Tinubu ya kuma yi fatan Allah Ya ba su nasarar gyara ƙasar nan. “Muna fuskantar ƙalubalen masu garkuwa da mutane, ƴan bindiga, da sauransu. Muna fatan Allah Ya mana rahama gaba ɗayanmu ya karɓi ayyukanmu na ƙwarai Ya nuna mana wata nagaba ya kuma ƙarfafe mu wajen kyautatawa”.

Shugaba Tinubu ya ja hankalin malamai da su zamto masu koyar da mutane muhimmancin yafiya, haƙuri, da ƙarfafa imani da kyauta a matsayinsu na waɗanda Allah Ya ba wa hikima da ilimin fahimtar da al’umma.

Daga ƙarshe, shugaba Tinubu yayi fatan Allah Ya kauda yunwa, ya ƙarfafi mutane ya ba su ikon jin-ƙan juna da son ƙasarsu”.

Back to top button
error: Content is protected !!