Kannywood
Shu’aibu Lilisco Da Zulaihat sun Sami Qaruwa, Sun Cika Shekaru 20 Da Aure
ALLAH ya albarkaci jarumi a Kannywood, Shu’aibu Idris Lilisco, da tsohuwar jaruma, Malama Zulaihat Ɗalhat, da ‘ya mace.
Zulaihat ta haihu ne a ranar Lahadi, 10 ga Disamba, 2023 da misalin ƙarfe 4 na yamma a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.
A Ranar Lahadi, 17 ga Disamba aka raɗa wa jaririyar suna Halima, amma za a riƙa kiran ta da Samha.
Zulaihat ta shaida wa mujallar Fim cewa bayan kwanaki uku da haihuwar, wato ranar Laraba, 13 ga Disamba, su ka cika shekara 20 da aure.
A yanzu dai ‘ya’yan su huɗu, amma haihuwa biyar, domin kuwa ɗaya ya rasu.
Allah ya raya su, ya kuma albarkaci rayuwar su.