Shirin Sayar Da Siminti A Kan Naira Dubu 3,500 Kowanne Buhu Ya Sami Cikas
Shirin Sayar Da Siminti A Kan Naira Dubu 3,500 Kowanne Buhu Ya Sami Cikas Ne Daga Dillalan Kasuwa, A Cewar BUA
Kamfanin ya bayar da karin haske ne biyo bayan wa’adin kwanaki 7 da wasu kungiyoyin farar hula biyu suka bayar ga mahukuntan kamfanin, inda suka bukaci a sayar da siminti a kan Naira 3,500 Kowanne buhu, Kamar yadda shugaban kamfanin Abdussamad Rabiu ya alƙawarta a bainar jama’a
Timothy Sogbeinde, wanda ke kula da Creatives & Visual Identity management a BUA Group, ya bayyana cewa, kamfanin ya shafe watanni yana siyar da siminti a kan Naira 3,500 kafin ya dakatar da Hakan.
Babban Daraktan kamfanin Alhaji Kabiru Rabiu ya ce, “A gaskiya mun sayar da simintinmu na tsawon watanni uku zuwa hudu a kan Naira 3,500. Mun yi tunanin sauran ’yan kasuwa a masana’antar siminti za su hada kai wajen samar da farashin siminti mai araha Amman abun yaci tura.