E News

Shin Wacece Zainab Ado Bayero (Jummai)

Zainab Ado Bayero (JUMMAI): Hannun Ka Ba Ya RUƁEWA Ka YanKe Ka Yar!

Mutane da dama sun yi mamakin ganin guntun bidiyon da na wallafa a shafi na a daren jiya na tsakuren hirar da gidan talbijin na TVC ya yi da Zainab Ado Bayero, wadda ta gabatar da kan ta a matsayin ɗiyar marigayi Sarkin Kano (Allah ya rahamshe shi, amin). Da yawa sun yi mamakin jin cewa ita ɗiyar Sarkin ce, har suna shakka, ba domin komai ba sai saboda irin shigar ta wadda ta saɓa wa al’adar Hausawa da Musulunci. Wani ma cewa ya yi shi bai yarda ‘yar Sarki Ado ba ce.

To, a gaskiya Zainab (Jummai) ɗiyar Takawa ce ta cikin sa. Mahaifiyar ta ‘yar ƙabilar Edo ce daga Jihar Edo. Sarkin Auchi ne kakan ta. Uwar ta ce Sarkin Auchi ya ba Sarki Ado riƙo, wato ya kula masa da ita, lokacin da ta je karatu a Jami’ar Bayero. Sarki Ado da ita sun haifi ‘ya’ya biyu, Zainab da ƙanen ta.

Zainab (Jummai) ta yi karatu a Ingila da nan Nijeriya. Yanzu mai shirya fim ce irin na tarihi da al’amuran yau da kullum, wato documentary.

Jummai ta zaɓi ta bi al’adar da ba ta Hausawa/Musulunci ba, musamman wajen shigar ta. Wannan zaɓin ta ne, kuma ba ka isa ka ce don ta yi shigar da ta saɓa da ta gidan su ita ba ‘yar gidan ba ce. Uwa-uba, ta ce ita Musulma ce kuma macen ƙwarai. Sannan ta yi kyakkyawar hulɗa da mahaifin ta.

Ba shakka, ‘yan gidan ba su jin daɗin lamarin ta kwata-kwata. A hirarrakin da ta yi da jaridu a baya, ta bayyana cewa sarakunan Kano da Bichi (wato waɗanda aka tuɓe kwanan nan) sun yi ƙoƙarin su hana ta yin fim ɗin da ta shirya game da tarihin mahaifin ta da gudunmawar sa ga ƙasa. Dalilin su, a cewar ta, shi ne saboda ita mace ce kuma uwa-uba ba ta bin al’adar gidan su wajen suturta jiki. Ta ce shi ya sa duk wanda ta tunkara domin ya taimaka mata sai ya ƙi.

A cewar ta, duk da zagon ƙasa da ake yi mata kan wannan shirin fim, ba ta karaya ba domin mahaifiyar ta da wasu mutane daga kudu sun ba ta ƙarfin gwiwa.

To, Zainab dai ‘yar Arewa ce ko mun ƙi ko mun so. Kuma ‘yar gidan Dabo ce. Fulani ce. Ko fuskar ta ka kalla ka san hakan ne. Saka ƙananan kaya da barin kai a buɗe ba su soke wannan cancantar ba. Ko ka ji wani ɗan gidan ya fito ya ƙaryata ta ne?

Abin da wasun mu ba su sani ba shi ne akwai ‘ya’yan Musulmin Arewa da yawa irin Zainab. Ni kai na na san su da ɗan dama, wato ‘ya’yan da waɗansu manyan Arewa (kai har ƙananan) suka haifa da wasu ƙabilu ko jinsi (misali Turawa ko Larabawa ko Canis) ko mabiya wasu addinan, kuma suka bi ɗabi’ar ɓangaren mahaifiyar su. Wani babba ɗin ma sai ya mutu sannan ake ganewa. Ana zaman makoki a gidan Bahaushe/Bafillace/Banufe/Kanuri, sai a ga Bayarabiya ko wani Inyamiri sun zo a matsayin ‘ya’yan mamacin. Sau da yawa, sai ka ga an hana su cin gado da ake rabawa – kamar yadda Zainab Ado Bayero ta ce an hana ta.

Lokaci ya yi da ya kamata mu rage tsattsauran ra’ayi kan faruwar irin wannan al’amarin. Ba laifin ‘ya’yan da aka haifa ba ne tunda ba su ne suka haifi kan su ba. Tilas mu rungume su a matsayin namu, domin ta haka ne za mu iya ɗora su kan hanyar da ta dace su bi, kuma mu rufa wa kan mu asiri. Kyara da tsana ko sharewa da kora ba su iya sauya lamarin su. Hausawa sun ce hannun ka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar!

Karanta waɗannan hirarrakin da ke ƙasa don samun ƙarin fahimta game da Zainab Ado Bayero:

Northern elites, emirs, are against my father’s biopic – Zainab Ado Bayero

Ado Bayero: Why I produced documentary about my late father — Zainab Ado-Bayero 

Zainab Bayero speaks on late emir’s legacy, Kano emirate tussle

Zainab Ado Bayero: Labarin ‘Yar Sarkin Kano da ta Bambanta da Jikokin Gidan Dab.

Docu-film on Ado Bayero screened at Freedom Park

Daga Ibrahim Sheme

Back to top button
error: Content is protected !!