Taurarin fina-finan Hausa, Aisha Ahmad Idris da aka fi sani da A’ishatulhumaira da abokin aikinta, Salisu Fulani kenan a wadannan kayatattun hotunan da su ka yi shugar Ango da amarya.
Bayan saka hotunan da A’Isha ta yi a shafinta na sada zumunta, wasu sun yi tsammanin aurene ta yi ko kuma suka yi da Salisu Filani.
Itama dai ta karawa wannan tunani karfi inda ta rika saka hotunan nata ita kadai da rubuta “Alhamdulillah”
A wani hoton kuma data saka ita kadai, Abokin aikinta, Abdul Ilyasu Tantiri yace mata” dama fa kince idan zakiyi aure saidai kawai a gani Allah ya bada zaman Lafiya”
Shima dai Salisu Fulani ba’a barshi a baya ba inda ya saka hotunansu tare ya kuma rubuta “Alhamdulillah”
A wani hoton da ya saka kuma ya rubuta cewa, “Masha Allah mun godewa duk wanda suka samu halarta”
Hakanan a wani hoton ya bayyana cewa “Aure Martaba, Alhamdulillah ”
Saidai hutudole ya fahimci cewa da wuya idan aurene taurarin fina-finan Hausa suka yi domin babu wata alama data tabbatar da hakan, babu wata kafa, musamman wanda suka shahara wajan kawo labaran Kannywood da ta ruwaito cewa aurene wadannan taurari suka yi. Sannan babu katin gayyata, hakanan babu wani abokin aikinsu daya taya su murna da cewa sunyi aure.
Sai Dai Mun fahimci cewa wadannan hotuna an daukesune lokacin daukar wani shirin fim, kamar yanda hakan ta taba faruwa a baya tsakanin, Saddiq Sani Saddiq da Rahama Sadau, Maryam Booth da Sadiq Zazzabi, Ali Nuhu da Hadiza Gabon a baya.