Kannywood

Shekaru Goma Cif Da Yin Auren Fati Ladan Da Shatima

Tsohuwar Shahararriyar Jaruma a Kannywood, Hajiya Fati Ladan, ta bayyana sirrin irin zaman da su ka yi da mijin ta har tsawon shekara goma zuwa yanzu. Kuma ta yi fatan Allah ya kash*ta a ɗakin mijin ta.

Fati Ladan

Fati ta yi waɗannan kalaman ne a hirar da ta yi da manema labarai dangane da cikar ta shekara goma cur a gidan aure a jiya Lahadi a gidan mijin ta a Kaduna.

Alhaji Yerima Shettima, shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum), shi ne mijin ta.

Fati da Yerima dai su na da ‘ya’ya biyu a tsakanin su, A’isha Humaira da Muhammad Shafi’u, kuma su na zaune ne a Kaduna. Fati ita ce amarya a cikin matan sa biyu. Ga yadda hirar ta kasance:

FIM: A zaman auren ku na shekara goma cur da mijin ki Yerima Shettima ba a taɓa jin ku da wata matsala ko tangarɗa ba. Menene sirrin?

FATI LADAN: Assalamu alaikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. Ina godiya sosai ga Allah (s.w.t.) da ya nuna min wannan babbar rana. Saboda shekara goma ba kwana goma ba ne.

Abin da zan iya cewa a shekaru goman nan da mu ka yi da maigida na, ba wani sirri ba ne illa kawai haƙuri da soyayya. Saboda idan akwai soyayya aka ce ba haƙuri, sai ka ga kuma ba za a kai ga cimma inda ake so a kai ba. To, haƙuri da kuma soyayya shi ne kawai sirrin.

FIM: Kasancewar tauraruwar ki ta haska a fagen shirin finafinai kafin ki yi aure, bayan auren ki, kin taɓa shiga damuwa kafin ki saba da zaman gidan miji?

FATI LADAN: Gaskiya ban taɓa shiga wata damuwa ba. Saboda a duk lokacin da mutum ya ce zai yi abu, musamman aure, to ina tunanin ba wasa ya je yi ba, aure abu ne wanda in har ka yanke hukuncin cewa za ka yi shi, ka san da sanin cewa ibada za ka je ka yi. A lokacin da na yanke shawarar zan je in yi aure, na sanya wa zuciya ta cewa zan je in zauna, ibada zan yi. Wannan abin da na sa wa rayuwa ta ya sa ban fuskanci wani ƙalubale dangane da zaman aure na ba ko in ji ina ‘missing’ ɗin wani abu ba. ‘In fact’ miji na ya na ba ni goyon baya ɗari bisa ɗari a dukkan abin da na ce zan yi; in dai bai saɓa wa addini na ba da al’ada ta zai ba ni goyon baya. Hakan ne ya sa na maida shi kamar aboki a wuri na, shi kuma ya maida ni ƙawa a wurin shi. Duk abin da za mu yi, mu na yin shi tare da ni da shi. Ban yi ‘missing’ ɗin wani abu ba, gaskiya, saboda duk abin da na ke nema ina samu a wurin miji na.

FIM: Me ki ka fi alfahari da shi game da kasancewar ki tsohuwar fitacciyar jarumar finafinan Hausa?

FATI LADAN: Abin da na fi alfahari da shi shi ne, abu ɗaya zuwa biyu. A duk lokacin da na wuce har yanzu, za ka ji an ce, “Ba ku gane ta ba, ai ita ce Fati Ladan, tsohuwar jarumar nan!” Wasu da dama za su zo su yi hotuna da ni, kuma na san cewa in ba albarkacin fim ɗin ba, babu yadda za a yi a san ni. To ina alfahari da wannan ɗari bisa ɗari.

FIM: Hajiya Fati, a bisa al’ada akasarin fitattun taurari idan su ka yi aure, su kan canza layukan wayoyin su saboda gudun damuwar masoyan su. Kin taɓa canza layin wayar ki?

FATI LADAN: E, na canza. Lokacin da za a yi aure na, miji na ya zo gidan mu, ya zo hira, waya biyu na ke da shi lokacin, sai ya ga ana yawan kira na duk bayan saƙwanni, to na fahimci kamar rashin gamsuwa a tattare da shi. Kwanaki kaɗan kafin auren mu sai ya ce in canza layi, sai na ce to ba komai. Haka ya faru, kafin bikin sai ya canza min duka layuka na.

FIM: Me ya fi burge ki game da zamantakewar ki tsakanin ki da mijin ki?

FATI LADAN: Abin da ya fi burge ni shi ne, mutum ne mai nuna soyayya sosai ga matar shi, ya na nuna soyayya ga iyalin shi gaba ɗaya. Saboda ya na da lokaci na musamman, duk da abubuwa na yi masa yawa, ya kan samu lokaci na musamman gare mu. Wannan na yi min daɗi ɗari bisa ɗari.

FIM: Akwai ce-ce-ku-ce da ake yi, wanda ke ma kin sani, wanda fitattun jaruman Hausa, sun yi ƙaurin suna ana cewa ai ‘yan fim ba su ma zaman aure. Menene kiran ki ga tsofaffin taurari da kuma sababbi?

FATI LADAN: Abin da zan iya ce masu shi ne dai su yi haƙuri, domin duk abin da za ka yi a rayuwar nan, in har ka na so ki cimma burin rayuwar ka, ka cimma nasara a kan inda ka dosa, sai ka yi haƙuri. Saboda ba ka taɓa ji an ce haƙurin mutum ya ƙare ba. Haƙuri halin Manzon Allah (s.a.w.) ne. Duk abin da za su yi, su san cewa mu na yin shi ne don Allah. Aure don Allah mu ke yin shi, kuma abin da ake nema lahira, bai zuwa da sauƙi. To a yi haƙuri a jure, sai an jure. Babu auren da ba shi da matsala a rayuwar nan ga baki ɗaya, amma in aka yi haƙuri sai a cimma inda ake so a je. Haƙuri dai shi ne ‘key’ ɗin komai. Kuma ina so su ba maraɗa kunya. Kamar yadda aka yi mana kuɗin goro, aka ce ba mu zaman aure, ba haka ba ne. Ni a tunani na ba auren ‘yan fim kaɗai ke mutuwa ba, amma da yake mu an san mu, dole za a riƙa yi mana kuɗin goro ana cewa ba mu zaman aure, amma mu na zaman aure. To ina so su yi haƙuri, su ba maraɗa kunya, a cimma inda ake so a je.

FIM: Akwai maganar da Bature ke cewa, ‘A general is always a general’, har yanzu misali; sha’awar harkar finafinai ya faɗo maki ko kuma a yi wa harkar fim wani abin da bai dace ba da zai taɓa industiri, abin na yi maki zafi? In alheri kuma ya same ta, ya na yi maki daɗi?

FATI LADAN: Ƙwarai kuwa. Inda alheri ya same ta ina jin daɗi, idan kuma aka yi wani furuci haka a kan wasu da su ka shigo daga baya haka, cewa ai yanzu industirin ta lalace, na kan ji ba daɗi, saboda ko an ƙi ko in so, ina daga cikin su. Don haka dole ba zan taɓa goge wannan sunan ba. Idan aka faɗi alkhairin ta, na kan ji daɗi, idan aka faɗi sharrin ta na kan ji ba daɗi. Amma maganar in ji ina sha’awar harkar fim, ba na yi, gaskiya. Daga lokacin da na ce na haƙura, na yi ritaya na aje, ko kuma na ba shi baya, ba wai don ba shi da wani abu ba, an yi gaba, an wuce. Aure na fuskanta, kuma ina fata Allah ya kashe ni a ɗakin miji na, shi ne fata na.

FIM: Irin riƙon da Alhaji Yerima Shettima ke maki kafin ki ka aure shi, kafin ki tare a gidan shi, ya yi maki bazata? Kin zaci cewa za a yi maki irin wannan riƙon kafin ki tare gidan sa?

FATI LADAN: Ni da miji na mun haɗu dududu ba mu yi wata huɗu ba, mu ka yi aure. Mafi akasarin soyayya ta da shi da kuma wata kula, sai a gidan shi na same shi, saboda ban san ma wanene shi ba lokacin da mu ka haɗu da shi. To ka ga a cikin wata huɗu, ba za ka iya fahimtar mutum ko wanene shi ba. Kawai abin da zan iya cewa, Allah ne ya haɗa ni da shi. Amma kular da na ke samu a gidan miji na, sai dai in ce na gode. Alhamdu lillahi.

FIM: Kun samu ƙaruwa?

FATI LADAN: Ƙwarai kuwa.

FIM: ‘Ya’yan ku nawa?

FATI LADAN: ‘Ya’ya uku. Biyu masu rai, ɗaya Allah ya karɓi abin sa.

FIM: Maza ko mata?

FATI LADAN: Mace da namiji. Akwai A’isha Humaira, akwai Muhammad Shafi’u.

FIM: Menene saƙon ki ga ɗimbin masoyan ki da abokan arziki?

FATI LADAN: Ina yi masu fatan alkhairi. Kuma ina miƙa saƙon godiya ta musamman a kan soyayya da su ke nuna min a lokacin da na ke waje da kuma yanzu da na ke cikin gida. Saboda akwai ‘comments’ da yawa da na ke gani, ina godiya sosai. Saboda alhamdu lillahi, ina farin ciki sosai, saboda ‘comment’ ɗin da na ke samu a lokacin da na ke industiri da yanzu, ‘comment’ ne mai kyau, saboda akasarin mutane da na ke ganin ‘comment’ ɗin su cewa su ke yi, “ku ku ka shiga industiri lafiya, kuma ku ka bar ta lafiya.” Wannan ya na yi min daɗi. Ina godiya ga masoya na. Kuma su ci gaba da taya mu addu’a., mu ci gaba da zama lafiya a cikin gidan mazajen mu, shi ne kawai abin da na ke so.

* A ranar 20 ga Disamba, 2023 in Allah ya kai mu Fati Ladan da mijin ta Yerima Shettima za su cika shekara goma cur da aure. An ɗaura auren su ne a ranar Juma’a, 20 ga Disamba, 2013 a ƙofar gidan su Fati da ke Unguwar Sarki, Kaduna.

Daga:- Fimmagazine.com

Back to top button
error: Content is protected !!