Kannywood

Shekaru 13 Da Auren Mu, Ina Alfahari Da Mata Ta

DARAKTA a Kannywood, Kamal S. Alƙali, ya bayyana matar sa Maimuna Aminu a matsayin wata jigo a rayuwar sa cikin tsawon shekaru 13 su ka kasance a matsayin ma’aurata.

Kamal, wanda kuma furodusa ne, ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da mujallar Fim dangane da bikin cikar su shekaru 13 da aure.

Ya ce shi da iyalin sa su na zaune cikin aminci da kwanciyar hankali.

Kamal ya ce: “A yanzu mun cika shekaru goma sha uku da auren mu, wanda aka ɗaura a ranar 25 ga Yuli, 2010, don haka a wannan lokacin mu ke bikin cikar mu shekaru goma sha uku domin nuna godiyar mu ga Allah.”

Ya kara da cewa: “Zaman mu da mata ta Maimuna Aminu abin alfahari ne, domin mace ce mai son addini don ta na da haddar Ƙur’ani. Sannan ta na da biyayya; duk abin da na hana ta ba za ta yi ba, don haka ina alfahari da ita a matsayin jigon rayuwa ta.”

Daga: Fim Magazine

Back to top button
error: Content is protected !!