Kannywood

Sharhin Fim Din Aliya Shiri Mai Dogon Zango

SHARHIN FIM ƊIN ALIYA: Fim Ɗin Aliya Fim Ne Da Aka Shirya Shi A Kan Tsarin Al’adun Bahaushe Da Tarbiyyar Addinin Musulunci, Fim Ɗin Cike Ya Ke Da Tausayi Da Ilmantarwa Da Wa’azantarwa Da Faɗakarwa.

Aliya shiri ne na musamman da aka shirya daidai da zamani wanda ya dace da al’ada da kuma addinin musulunci. A cikin fim ɗin an nuna yadda rayuwar ƴan mata marasa gata ta ke kasancewa inda su ke shan azaba da wahala wadda tauraruwar shirin (Aliya) ta sha.

Fitaccen Darakta Hassan Giggs shi ne ya shirya tare da ba da umarnin shirin. Shirin bai ci karo da al’ada da koyarwar addinin musulunci ba, ya dace da al’adun Hausawa da koyarwar addininmu na musulunci. Malamai da dattawa duk za su iya haɗuwa su kalla.

Shirin ya sha bamban da fina-finan da aka saba shiryawa a wannan zamani waɗanda su ke cike da kwaikwayon al’adun turawa da Indiyawa, a wannan Fim mai suna (Aliya) an fito da zallar al’ada da hawar da Fim ɗin bisa kan tsarin addinin musulunci.

Fim ɗin Aliya na cike da tausayi, ilimantarwa, wa’azantarwa, faɗakarwa, tunatarwa. Sannan kuma, Fim ɗin zai ƙarawa duk wani mai imani imani ya kuma sanya imani a zuciyar marar imani tayadda mutane musamman zaman iyali za su guji gallazawa wani ko wata cikin zamantakewa saboda gudun ƙarshe marar kyau.

Sannan Fim ɗin zai sanya haƙuri da tawakkali a zukatan duk wasu waɗanda su ke cikin wata jarabawa ta rayuwa su yi haƙuri har zuwa lokacin da Allah zai kawo musu mafita. Kamar yadda darakta Fim ɗin ya nuna, Aliya ta sha wahala a Fim ɗin amma daga ƙarshe ta ci ribar haƙuri da juriyar da ta yi.

Ku ziyarci shafin YouTube ko nemi Fim ɗin Aliya ku ba wa Idonku abinci, kuma ku ɗauki darusan da ke cikin Fim ɗin. Shiri ne mai dogon zango wanda zai riƙa zuwa muku sau ɗaya a kowane mako.

Back to top button