Shaikh Pantami Ya Roki Matashin Da Ke Masa Matattaki Ya Dakata
Shaikh Pantami Ya Roki Matashin Da Ke Masa Matattaki Ya Dakata
Wani matashi mai suna Auwal, ya nufi garin Abuja daga Gombe akan keke don girmamawa ga Prof. Isa Ali Pantami. Inda ya wuce ta Alkalerin jihar Bauchi a yau Litinin.
Sai dai bayan da Shaihin Malamin ya sami labarin yunkurin matashin, ya roke shi da ya tsaya a Bauchi domin kare lafiyarsa.
Shaihin Malamin ya rubuta a shafinsa na facebook kamar haka;
“Allah Ya kara mana kaunar juna. Allah Ya saka da alheri Dr Yakubu Sani Wudil da ka ankarar da ni kan wannan abu.
“Ina rokon Malam Auwal ya tsaya daga Bauchin, a gidana dake gefen Masjidul Qur’an a inda za’a karbe shi sannan kuma a gana da shi a matsayina, sannan a karrama shi. Kare lafiyar sa, da rayuwar sa da mutuncinsa abu ne muhimmi a gare ni.
“Daga baya sai a sa shi a mota tare da keken sa zuwa Gombe. Muna godiya sosai, Allah Ya biya shi da gidan Aljannah.” In ji Farfesa Shaikh Ali Isa Pantami.
Ku taimaka kuyi sharing ko sakon ya kai ga matashin.