Kannywood

Shagalin Sallah Daga Gidan Ali Nuhu

Hotunan Shagalin Sallah Daga Gidan SarKi Ali Nuhu, Da Gidan Lilin Baba Angon Ummi Rahab! Shima Jarumi Ali Nuhu Ya Tabbatarwa Da Jama’ar Duniya Cewa Yayi Sallah Lafiya, Inda Ya Wallafa Wasu Hotuna Da Bidiyo Tare Da Iyalansa, Matarsa Maimuna, Da Yaransa. Ahmad Ali Nuhu, Fatima Ali Nuhu.

Alamu Ya Nuna Ali Nuhu Yana Cikin Jin Dadi Da Kwanciyar Hankali Tare Dashi Da Iyalan Nasa, Shima Daga Bangaren Sabon Ango Lilin Baba Ya Wallafa Hotunansa Tare Da Amaryarsa Ummi Rahab, Inda Suma Su Fito Suyi Kyau Gwanin Sha’awa.

Daga Dayan Bangaren Shima Sabon Ango Abubakar Bashir Maishadda Ya Wallafa Hotunansa Tare Da Sabuwar Amaryarsa Wato Hassana Muhammad, Sai Kanninsa Mata Guda Biyu.

Sauran Jaruman KannyWood Suma Ba’a Barsu A Baya Ba, Inda Da Yawansu Sun Bayyana Hotunan Nasu Tare Da Na Iyalansu. Dama Ance Sallah Mai Yawan Ado, Muna Fatan Allah Ya Karba Ibadu, Ya Kuma Maimaita Mana Cikin Dai Da Koshin Lafiya Amin.

 

Back to top button
error: Content is protected !!