Labarai
Sarkin Bichi Ya Tsige Kawunsa Daga Sarauta
Sarkin Bichi Ya Tsige Kawunsa Daga Sarauta
Daga Habibu Aja’waya Dawakin Dakata Kano
Masarautar Bichi karkashin Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauke kawunsa, wato Alhaji Idris Bayaro Barden Kano, wanda kanin Sarkin Kano Alhaji DR Ado Bayero ne. Kuma Dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero Jikan Sarkin Kano Abas.
Inda ya maye gurbinsa dan uwansa wato Alhaji Abdulhamid Ado Bayaro a matsayin sabon hakimin Bichi.