Labarai

Sako Daga Masoyan Dauda Rarara Zuwa Ga Gwamnati

Sako Daga Ƙungiyar Mmasoya Jam’iyyar (APC) Da Kuna Alhaji Dauda Kahutu Rarara Na Kasa Zuwa Ga Gwamnati.

“Muna kira zuwa ga dukkan shugabaninmu na jam’iyyar (APC) tun daga kan fadar shugaban ƙasa har zuwa matakin Jihohi da su yi gaggawan yin abin da ya dace cikin kwana 4 kacal domun ganin mahaifiyar Alhaji Dauda kahutu Rarara ta dawo gida cikin kwanciyar hankali.

Domin Alhaji Dauda Kahutu Rarara shi ne Jam’iyyar (APC) duba da irin gudumawar da yake ba ta.

Mun zuba Ido mu ga me za a ba wa Alhaji Dauda kahutu Rarara a gwamnatinmu ta APC amma ba mu shaida komai da aka bashi ba, ba minista ba SA, ba komai.

Yau kuma an sace mahaifiyarsa kusan sati guda kenan ba mu ji wani jigo a gwamnatinmu yace komai ba.

Gaskiya ba za mu yarda mu zuba Ido mu ga haka ba.

Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya fi ƙarfin a yi amasa haka. Ba ma goyon baya mu masoyan Jam’iyyar (APC).

Allah yafitar da hajiya daga hannun ɓatagari lafiya, Amin”.

Back to top button
error: Content is protected !!