Kannywood
Sadiq Sani Sadiq Suna Murnar Cika Shekaru 7 Da Aqure
Tauraron fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq da matarsa, Murja Shehu Shema na murnar cika shekaru 7 da yin aure.
An daura auren Sadiq sa masoyiyarsa, Murja wadda kanwace ga tsohon gwamnan jihar Katsina, Barisra Ibrahim Shehu Shema ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2013.
Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya biyu mace da Namiji.
A sakon daya fitar ta shafinshi na Instagram,Sadiq ya bayyana irin soyayyar da yakewa matar tasa inda yace,idan babu ke babu Rayuwa, ina godiya da kika shigo cikin rayuwata.
Muna taya su murna da fatan Allah ya kara dankon soyayya.