Kannywood

Sabuwar Bidiyon Murja Ibrahim, Tare Da Lilin Baba Da M Shareef

Daga Wajen Daukar Sabon Bidiyon Wakar Lilin Baba Da M Shareef Tare Da Murja Ibrahim (‘Yar Tiktok) Murjan Dai Kamar Yadda Aka Santa A Shafin Tiktok, Tana Daya Daga Masu Bada Nishadi. Sannan Kuma Kwararriyace A Wajen Hawa Bidiyon Wakoki.

Tana Fitowa Cikin Wakokin Bidiyo Na Hausa, Wannan Karon Da Alamu Zata Fito Cikin Wani Sabon Bidiyon Wakar Lilin Baba Da Umar M Shareef Ne, Inda Ake Sa Ran Ba Da Jimawa Ba Zata Fito,

Dun Daga Wajen Aikin Bidiyon Wakar, Jarumar Ta Fara Barkwanci, Inda Tasa Kusan Kowa Dariya, Dama Kuma Kowa Yasan Murjan Wannan Aikinta Ne Wajen Sa Mutane Nishadi.

https://youtu.be/Ofk6_6mSsyA

 

One Comment

Back to top button
error: Content is protected !!