Labarai

Rundunar Sojojin Nigeria Ta Ceto Mutum 8 Daga Hannun Yan Ta’adda

RUNDUNAR HADARIN DAJI TA CETO MUTANE 8 DAGA HANNUN ‘YAN TA’ADDA

A kokarinta na tsaftace gonakin noman rani fadin Arewa maso yamma, Rundunar Hadarin Daji (OPHD) ta sake samun nasarar fatattakar ‘yan ta’addan wasu muhimman yankuna na jihar Zamfara.

Har ila yau sojojin sun yi nasarar ceto mutane 8 da aka yi garkuwa da su da kwace muggan makaman ‘yan ta’addan

A yau, 28 ga Fabrairu, 2024 sojojin OPHD suka ci gaba da dannawa yankin Bayan Ruwa wanda ake zargi da zama.babban tudun-mun-tsira ga ‘yan ta’adda a jihar a wani kazamin fada da aka gwabza tsakanin sojojin da ‘yan ta’addan inda sojojin suka sami galabar ceto mutane 8 din ba tare da sun sami ko da kwarjane ba, kana suka lalata yankunan da ‘yan ta’addan ke samin mafaka tare da kwace iko da yankunan

Tuni dai an mika dukkan wadanda aka ceto ga hukumomin da suka dace domin hada su da iyalansu.

Daga Lt. Suleman Omale,
Jami’in Watsa Labarai na rundunar, Fabrairu 28, 2024

Fassarar Rahma Abdulmajid.

Back to top button
error: Content is protected !!