Kannywood

Rasuwar Bintu ‘Ɗaɗin Kowa’ Ta Girgiza KannyWood

Rasuwar Bintu ‘Ɗaɗin Kowa’ Ta Girgiza KannyWood

A Ranar Lahadi Allah ya ɗauki ran jarumar Kannywood, Fatima Sa’id Yakasai, wadda aka fi sani da Bintu a cikin shiri mai dogon zango na ‘Ɗaɗin Kowa’ na tashar talabijin ta Arewa 24.

Matashiyar jarumar mai kimanin shekara 25 a duniya, ta rasu da misalin ƙarfe 2:00 na rana, bayan fama da doguwar jinya da ta yi.

An yi jana’izar ta a unguwar Gunduwawa da ke Kano.

‘Yan fim sun yi jimamin rashin Fatima, duk inda ka leƙa soshiyal midiya hotunan ta ke yawo tare da yi mata addu’ar neman rahama.

Daga Fimmagazine.com

Back to top button
error: Content is protected !!