Kannywood

RASHIN HIKIMA A DA’AWA YA SANYA AN MAYAR DA BATANCI ZUWA WA’AZI KO KUMA NASIHA

RASHIN HIKIMA A DA’AWA YA SANYA AN MAYAR DA BATANCI ZUWA WA’AZI KO KUMA NASIHA

Game Ta takaddamar Rahma Sadau
Ina mai kwadaitar da mai karatu, ya karanta wannan kissa mai cike da Al’ajabi na wani Sharifi, ,Mujahidi, wanda Sheikh Muhammd Aslam ya nakalto irin salon da yake bi wajen yada da’awa.

Sheikh Shariff Habib Ahmad (R.t.a) ya shigo harkar da’awa Africa ta gabas tun a shekarar 1347 (H) wanda yayi dai-dai 1928 (M), wata rana Ahmad yaje wani kauye, sai ya kira al’ummar kauyen zuwa ga Addini, sai Dagacin kauyen yace da shi “eh, ya amince zai karbi Musulunci amma ba zai iya yin sallah ba, sai Sheikh Habib yace dashi kace “La’ilaha’iallahu Muhammadar-Rasu
lallah” kuma kada ka damu, sai ya furta kalmar shahadar ya shiga Addinin Musulunci da sharadin bazai iya yin sallah ba.

Shigar sa Addinin Muaulunci da wasu yan kwanaki, sai ranar sallar idi ta karato sai Sheikh Habib ya gayyaci wannan Dagaji da yazo ayi murnar wannan rana tare dashi, yace dashi “rakao’ine guda biyu kawai zakayi, ka dan motsa jini, kuma ka samu nishadi, sannan sai mu wuni muna shan liyafar wannan rana, sai dagacin kauye ya amince, ko da yazo sai aka tarbe shi cikin karramawa, aka sallaci idi dashi ya nishadantu da wannan rana nishadantuwa wajen bukukuwa, ciye-ciye da shaye shayen kayan marmari.

Bayan wani lokaci sai Sheikh Habib Ahmad ya kuma gayyatar sa, zuwa sallar juma’a, sannan yace dashi ” shima dai babu wahala, raka’o’ine guda 2 kamar sallar idin chan, sai Dagacin kauyen tare da jama’ar sa suka zo suka sallaci jumma’ar kuma aka shirya musu liyafa mai kayatarwa suka nishadantu sosai, sai ya kasance duk wani sati idan ta kewayo tare dashi ake sallatar Jumma’a.

Bayan wata 1, Sheikh Habib yace dashi ” yazo sallar magrib mana, domin ita da raka’a guda ta d’ara sallar idin chan da kuma sallar juma’ah, sai wannan shugaban kauye ya samu halarta kuma aka shirya masa liyafa ya nishadantu sosai, hakan ya sanya kullum tare dashi ake yin sallar magriba, sallar juma’a a sati, da kuma sallar idi a shekara.

Bayan shafe wani lokaci sai ga Shugaban kauye yana riga kowa zuwa halartar sallolin khamsu salawat gabaki daya, ba tare da wata kasala ba.

Mu duba irin wannan salo na hikima da fasaha da wannan malami yabi wajen Musuluntar da Dagacin wannan kauye tare da jama’ar sa, kuma an ce a irin wannan salo ya musuluntar da mutane samada dubu 300, kaga wannan salo shine irin salon da ALLAH yayi kira ga musulmi da su dinga mu’amalantar Addini dashi tsakanin su da wadanda ba musulmi ba, da kuma wadanda suka kauce hanya acikin musulmi.

ﺍﺩْﻉُ ﺇِﻟَﻰٰ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺭَﺑِّﻚَ ﺑِﺎﻟْﺤِﻜْﻤَﺔِ ﻭَﺍﻟْﻤَﻮْﻋِﻈَﺔِ ﺍﻟْﺤَﺴَﻨَﺔِ
Amma gashi Mu Musulmi, wahabiyawa sunzo sun gurbata tunanin mutane, kowa cikin bincikar aibu yake, yana sauraron dan uwan sa musulmi ya aikata wani kuskure ya fito yana zagin sa, aibata shi, da kokarin tsine masa, Alhali ALLAH ne kadai yasan abin da wasun mu ke aikatawa a boye, kuma ba’a bayyana tarin alkairan jama’a.

sai ka samu mutum bai silar shigo da ko mutum guda cikin Musulunci ba, amma kullum kokarin kore na cikin sa yake da sunan wa’azi ko kuma nasiha.

Yakamata mu gane bambanci tsakanin nasiha, wa’azi da kuma aibatawa, domin dayawa wasu na aibata musulmi ne, da kara kora su zuwa ga aikata alfasha da sunan wa’azi ko kuma nasiha.

Wannan baiwar ALLAH da ta aikata wannan abu, ko ba komi musulmace, sannan idan ma mutum baida hanyar da zai iya isar mata da nasiha, to kawai yayi mata addu’ar shiriya, tunda ANNABI (SAW) yace “Afadi alakiri ko ayi shiru”.

SANARWA. Ba ina goyon bayan abinda ta aikata bane, a’a laifin ta daidai yake da laifin masu aibatata, domin ALLAH yayi hani da muzanta halitta.

MUNA ROKON ALLAH, YA SHIRYE TA, YA GANAR DA ITA TA DAINA IRIN WANNAN MUMMUNAR SHIGA SANNAN YA BATA MIJIN AURE NAGARI TAYI AURE TA HUTA DA WANNAN RAYUWA MAI CIKE DA HADARI.

ALHAMDULILLAH.

Back to top button
error: Content is protected !!