Kannywood

Rashin Hakuri Ne Ya Sa kannywood Ta kasa Samun Cigaba – Hamisu Iyantama

Rashin Hakuri Ne Ya Sa kannywood Ta kasa Samun Cigaba – Hamisu Iyantama

Daya daga cikin manya kuma jagororin masana’antar kannywood Alh Hamisu Iyantama ya bayyana rashin jindadinsa na yadda aka kasa samun hadin kai da kuma hakuri domin samun cigaba a masana’antar fim ta Kannywood.

Madogara: Northflix
Jarumin yace “masana’antar kannywood ba ta rasa komai ba sai hadin kai, domin ta na da masana ta kowanne fanni da kuma hanyoyin kasuwanci.

Misalin daya shi ne kafar sadarwa ta northflix da aka bullo da ita, sannan kuma yaranmu, qannenmu da kuma abokanan mu su na da kwarewa kwarai da gaske. Sai dai maganar kasuwa ce da babu, kuma ba komai ya jawo hakan ba face rashin hadin kai da kuma hakuri da ba mu da shi”

Jarumin ya qara da cewa “ni da kaina na jagorancin gyara tsofaffin sinimu saboda wannan matsalar wanda kuma har yanzu tsarin yana nan kuma alhamdulillahi anyi yarjejejiya an saka hannu cewar duk wanda ya yi fim zai iya kaiwa wajen domin kofa a bude take matukar mutum ya cika qa’i’dojin da a ke yi domin fitarwa tare da haska fim a garin kano.

Kuma maganar fita garin kano na munyi yunkuri amma bamu qarasa ba saboda matsalolin da suka addabi kowa na rashin kudi domin hukuma ta kafa mu amma ba ta bamu kudin da zamuyi wannan aiki ba sai a aljihunmu mu da muke kishin wannan sana’a muke wannan yunkuri illa dan abinda ba a rasa ba.”
Mal Hamisu Iyantama ya fadi haka a lokacin da wakilinmu yake tattaunawa dashi kan al’amuran da suka Shafi kannywood inda ya ke tambayarsa a matsayin sa na babba kuma daya daga cikin jagororin kannywood ko akwai wani abu da su ke kokarin bullo da shi wajen inganta masana’antar
Jarumin ya qara cewa “ maganar gyara munyi kokari illa wasu daga cikinmu da ba su bada hadin kai da goyon baya ba.

Akwai wadanda su ke bi gari gari suna samun abinci da fina-finan da wasu nasu ne wasu kuma ba nasu ba ne. Sannan mun yi iya kokarin mu wajen ganin cewa an samu fahimta tsakaninsu da masu fina-finan amma abin ya ci tura, wanda har qara an kaimu a kan yunkurin ganin cewar masu satar fasaha anyi maganin hanyar da su ke bi.

Dani da kwamishinan ‘yansanda da shugaban hukumar tace fina-finai da makamantan mu ka zauna akan a tsaya a bi hanyar da it ace zata kawo gyara a cikinmu.

Sannan kafin northflix akwai online app da muma mu ka qirqira don habaka kasuwancin shima platform ne. Kuma munyi subsidizing dinsu su ‘yan piracy mun gayyaci kwamishinan ‘yan sanda, SS, ‘yan jaridu, da prison service da su kansu ‘yan piracy an koya musu sanin cewa su bi doka da Oder don ganin irin illar da take haifarwa tattalin arzikin Kasa da kuma masu harkar fim din.

Wannan shine gyara da mu ka tsaya mu ka yi kuma indai ba a bi wannan gyara da kokari da mukayi a baya ba to gaskiya ba gyara ‘yan fim din su ke so ba.” In ji Iyantama

Ya kuma rufe da cewa “Don haka mun yi iya yin mu kuma mun share musu fage domin ni kaina akwai fim dina da na kai sinima an kuma haska a Ray sinima da eldrado. Duk da babu wani kudi sosai sai dai idan aka jure zuwa gaba Insha Allah za a samu abin da ake bukata.”

Back to top button
error: Content is protected !!