E News

Rara Ne Gwarzon Matasa A Shekarar 2023

DAUDA RARARA KAHUTU NE GWARZON MATASA A SHEKARAR 2023 – INJI ABDULLAHI AL-HIKIMA

An zabi fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, a matsayin gwarzon matasan Arewacin Nijeriya, duba da irin ayyukan alheri da kuma abubuwan da ya shuka na ci gaba a wannan shekara ta 2023.

Kadan daga cikin abubuwan da Rarara ya yi daga farkon shekara zuwa karshenta sun hada da taimakawa matasa masu kananan sana’oi da kari domin su dogara da kan su, ya kuma taimaki masu amfani da kafafen sada zumunta (‘Yan Social Media) da kudade da kuma abubuwan hawa tare da manyan wayoyi

Haka zalika a kowace shekara ya kan bada gudummuwar abinci da kudade a cikin watan Ramadan ga masu karamin karfi da kuma ‘yan masana’antar shirya Finafinan Hausa.

Bugu da kari ya tallafawa matasa musamman daliban jami’a sama da mutum 160 da kudin Registration.

Rarara bai tsaya anan ba, ya tura wakilansa a wannan shekara ta 2023 in da su ka kai tallafin kayan abinci a gidan Marayu da ke jihar Bauchi. Wadannan kalilan ne daga cikin ayyukan alherin sa.

Muna rokon Allah yasa wannan shekara da za a shiga ta 2024 ya ninninka ayyukan alheri fiye da wanda ya yi a shekarar 2023 kamar yadda Al-hikima ya bayyana.

Me zaku ce?

 

Back to top button
error: Content is protected !!