Kannywood

Rainin Wayone Kawai Hadiza Gabon Tayima Amina Amal – Nafisa Abdullahi

Ran Nafisa Abdullahi Ya Baci A Lokacin Datayi Ido Biyu Da Abinda Hadiza Gabon Tayima Amina Amal Nafisa Tace Kawai Dan Taga Bazata Iya Ramawa Bane Shiyasa Ta Wulakantata A Idon Duniya Ba Kuma Tasan Cewa Daukaka Ta Karama Amina Amal Ba Nagisa Ta yi rubuce-rubuce da yawa kamar haka:
Nafisar tace ba zata taba goyon bayan cin zarafiba ballan tana idan taga ana rainin wayau. Tace Da Hadiza Gabon  ina kamun kan da nutsuwa da kikewa nunawa Duniya cewa kina dashi, ina kirkin da kike nunawa Duniya cewa kina dashi? a hakane zaki tabbatar da gaskiyarki ta hanyar cin zarafin Wannan Yarinyar?

Da ace kowa irin wannan hanyar yake bi wajan neman hakkinshi da kema baki tsira ba, saboda ba zaki so a miki haka ba ko wannan ba zai sa ki sassauta ba? Ke kina son ki kare mutuncinki amma ita kin sakata a Idon Duniya kina cin nata mutuncin, shin wama ya baki damar dukan mace ‘yar uwarki, saboda kina ganin cewa ita ba komai bace ba? Wasu mutanen na rayuwar karya amma basu sani ba cewa abinda suke aikatawa yana nunawa Duniya ainihin kalarsu.

Ta kara da cewa duk me cin mutuncin wani/duka yana jin dadi to mutumin banzane azzalumi, kuma ban zargi kowa ba sai ita Aminar  data maida kanta banza bata rike kimar kanta ba, ita data dauka mutum ake kaiwa kuka ba Allah ba…

Back to top button
error: Content is protected !!