Kannywood

Rahama Sadau Ta Fito Tana Kuka Tana Bada Hakuri

Jaruma Rahama Sadau Ta Fito Tana Kuka Tana Neman Gafara Akan Abun Da Hotunanta Su Jawo.

Ta Fitar Da Videon Ne A Shafinta Na Sada Zumunta Tare Da Wani Sanarwa Kamar Haka

Salam Alaikum Jama’a. • Na yi wannan video din ne cikin nadama da takaici. Ina kuma mai ba da hakuri bisa abin da ya faru ga dukkanni Hausawa, abokan aikina da musulmai baki daya bisa wannan hoto nawa da ya jawo wannan cece-ku-ce.

Wannan ba dabi’a ta ba ce a matsayina ta musulma. Ni masoyiyar Manzon Allah (SAW) ce, kuma Ina yaqi da duk wani wanda ya taba shi ko ya taba addinina. Kaddara ce ta kawo kawo har wani yayi batanci akansa Akan hotona. BANA TARE DASHI, Allah kuma ya la’ance shi Akan wannan batanci da husuma daya tayar a Lokacin da duniya ke cikin wani Hali . Haka ba zai kara faruwa a kai na ba insha Allah.

Na gode Allah ya kare mana imanin mu da addinin mu. 

Rahama Sadau❤️

 

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng

One Comment

  1. Tom kinsan shi Allah dazuciya daman yake aiki idan har tuban naki yasaki nadama tom bamakawa shi Allah Mai yafiyane akan kowace halitta tasa idan yaso.
    Shawara ta gareki don Allah kidaina daukar kanki tamkar wata baturia kina aikata Al,adunsu wannan shine abu mafi muni arayuwarki baki daya wlh. Sabida bawai muna yin karatun bokone domin muzama kamarsuba sae dan musami hujjar karekanmu daga sharrinsu.Ngd🙏 Allah yadatar damu baki daya.

Back to top button