Kannywood

Rahama Sadau Ta Caccaki KannyWood Kan Safara’u

Korar Da Akayiwa Safara’u Daga Masana’antar KannyWood Shine Sanadiyyar Gurbacewar Tarbiyyarta – Inji Rahama Sadau

Rahama Sadau Ta Caccaki Masana’antar KannyWood Kan Korar Da Akayiwa Tsohuwar Jaruma A Masana’antar KannyWood Safiyya Yusuf Wacce Akafi Sani Da Safara’u Yanzun Ta Dawo Safaa,

Kwanakin Baya Ne Shafin BBCHausa Suyi Hira Da Tsohuwar Jarumar Inda Ta Bayyana Halin Data Tsinci Kanta Kan Bayyana Da Bazuwar Bidiyon Tsiraicinta A Shafukan Sada Zumunta.

Hirar Da Akayi Da Jarumar Lamarin Ya Jawo Cece Kuce, Inda Mutane Da Dama Ke Tofa AlbarKacin Bakinsu Kan Afkuwar Lamarin.

Sai Dai A Wani Hira Da Akayi Da Jaruma Rahama Sadau, Ta Bayyana Alhakin Gurbaceear Tarbiyyar Safara’u Kan Masana’antar KannyWood, Inda Tace Inda Ace Lokacin Da Bidiyon Safara’u Ya Bayyana, An Kirata An Hukuntata To Da Kila Bata Fada Halin Da Take A Yanzun Ba.

Inda Rahaman Ta Kara Da Cewa Ba Safara’u Kawai Ba.. Yakamata Ace Idan Wani Ko Wata Sunyi Wani Abu Da Bai Dace Ba. A Kirashi Ko A Kirata Ayi Hukunci Akai, Domin Korar Da Akeyi Ba Shi Bane Mafita. Korar Shine AB Dake Kara Jagula Lamarin.

Ta Bayyana Cewa A Yanda Ta Dauka, Ta Dauki Kamar Cewa Wannan Masana’antar Tasu Ta KannyWood Kamar Yan Gida Daya Ne. Yayin Da Wani Yayi Ba Daidai Ba. Kamata Yayi A Gyara Masa Tare Da Hukunta Shi.. Amma Korar Da Akeyiwa Wasu Jaruman Bashi Bane Mafita.

https://m.youtube.com/watch?v=L2CtuAN-irQ

Back to top button