Kannywood

Rahama Sadau Nashan Suka Kan Musabaha Da Kashim Shetima

Jarumar KannyWood Rahama Sadau, Na Ci Gaba Da Shan Suka Kan Musabaha Da Tayi Da Mataimakin Shugaban Kasar Nigeria Kashim Shetima Yayin Kai Masa Ziyara Da Jaruman Na KannyWood Suyi.

KOWANE TSUNTSU KUKAN GIDAN SU YA KE YI

Daga Murtala Dan Talaka Magazu

Yabon gwani ya zama dole!
Wannan da ku ke gani sunanta khadija Abdulhameed, yarinyar taki gaisawa da Namiji bayan ta lashe gasar rubuto na kasar Najeriya.

In zaku tuna, UBA Foundation Nigeria National Essay Competition ta gudanar da gasar rubuto inda AbdulHameed Khadija Husna daga jihar Kano tayi na farko.

Bayan wannan gasar, Alkalin gasa yayi yinkurin gaisawa da Khadija domin ya tayata murna amma taki bada hannu don ta kare martabar ta amatsayin na musulma.

Ya kamata mata musulmai suyi koyi da wannan Yarinyar don kare mutuncin kansu a koina, Kuma da hakan suna nuna karantarwan addini.

Wane irin fata za ku yi mata?

📷 From Dantalaka Magazu

Back to top button