Rabuwar Aure Ba Maslaha Bace Duk Girman Laifi
Rabuwar Aure Ba Masalaha Ba Ne Duk Girman Laifi In Dai Ba Kisan Kai Bane.
DAGA: Bilkisu Yusuf Ali
“Ni dai a ra’ayina ban taɓa kallon rabuwa/saki a matsayin maslaha ta aure ba, musamman Idan da yara a tsakani kuma kowanne hali ne da mijin ko matar. In dai ba kisan kai ɗaya ke kokarin yi ba.
Al’ummarmu a yau sun bar aure ne a hannun ma’aurata kaɗai. Ba a sulhu, ba a tsawatarwa sannan uwa uba su kansu iyaye sun yi sake ƴaƴa ba sa tsoron su. In Kuma har Hakan ta faru ta rashin tsoron magabata to ai a dangi ba a rasa wani babba da ake tsoro ko don shekaru ko don iya jagoranci ko don zafinsa ko don hikimarsa da iya sulhu da iya magana ko Kuma don kuɗinsa ba.
To irin wadannan ma ana kai musu sulhun aure a da amma a yanzu in ma’aurata suka Sami saɓani ba me iya tsawatarwa. Sai bayan an rabu kuma duk a shiga ruɗani. Yara su shiga tangal-tangal, tarbiyyarsu ta lalace ko ita uwar a bar mata nauyin yara aka dole in har ba ta da sana’a ba ta da matallafi ba yadda ta iya sai dai ta zama karuwa.
Allah Ya kyauta. A ganinku ya sulhun aure ya kamata ya kasance ?”.