Labarai

Qungiyar Izala Ta Umurci Ayi Alkunutu A Masallatai Don Neman Sauƙi A Najeriya

Izala Ta Umurci Ayi Alkunutu A Masallatai Don Neman Saƙi A Najeriya

Ƙungiyar JIBWIS ta tarayyar Naijeriya ta bada Umurni ga Limamai da a fara addu’oin Al-ƙanut a dukkan masallatai na Juma’a da khamsul salawat.

Umurnin hakan ya fito ne kai tsaye daga bakin shugaban ƙungiyar Sheikh (Dr) Imam Abdullahi Bala Lau a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma’a a masallacin Umar Ɗan Haɗɗabi dake helkwatar kungiyar a unguwar Utako dake birnin Abujan Naijeriya.

Sheikh Bala Lau yace, za’a gudanar da addu’oin ne domin neman taimakon Allah da ya kawo mana zaman lafiya a kasar mu, da kuma karshen kashe-kashen ta’addanci da ya addabi arewacin kasar, da samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Kazalika Shugaban na JIBWIS ya umurci dukkan shugabannin kungiyar a matakin jahohi da su bada umarni ga dukkan masallatayyan dake jahohin su, da Malaman kungiyar da su duƙufa da addu’oi a cikin masallatai, makarantu da sauran wuraren Ibada domin neman Allah ya kawo mana saukin abubuwan da suka damemu a ƙasar.

A ƙarshe shugaban ya rufe da jan hankali ga al’ummar musulmi cewa kowa yasan abun da yake aikatawa na daidai ko akasin haka, yanzu lokaci ne da kowa zai tuba daga aikata saɓo, domin Allah ya dubi lamuran mu, ya sauƙaƙa mana rayuwar da ta mana tsada.

Allah yasa mu dace. Amin

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Back to top button
error: Content is protected !!