Obasanjo Yayi Tir Da Salon Tinubu Na Cire Tallafin Manfetir
Obasanjo Yayi Tir Da Salon Tinubu Na Cire Tallafin Manfetir
Tsohon shugaban ƙasa cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa waɗanda ke cin gajiyar sana’ar shigo da mai za su yi ƙokarin daƙile matatar man Ɗangote.
Obasanjo ya bayyana haka ne a sakamakon zargin da Ɗangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi na cewa wasu ‘Yan Mafiya na ƙoƙarin kawo cikas ga matatarsa da aka gina kan Dala biliyan 20.
Tsohon Shugaban kasar ya kuma yi Allah-wadai da salon da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin man fetur, inda ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati mai ci ta fara duba irin wahalar da tallafin zai iya jawowa mutane da kuma yadda za a gyara.
“Akwai ayyuka da yawa da ya kamata a yi, ba wai kawai ka tashi da safe ka ce ka cire tallafin ba, saboda hauhawar farashin kayayyaki, tallafin da muka cire bai tafi ba, ya dawo,” in ji tsohon shugaban ƙasar.