IyalaiLabarai

Nima Ina Neman Yaro Matashi Da Zan Aura.

Bayan auren da tauraron fim din Kwana Casa’in da Tara wanda tashar Arewa24 ke nunawa, Abdul yayi na wadda ta darashi da shekaru, lamarin ya dauki hankula sosai inda akaita samun mabanbanta ra’ayoyi.

Wasu ma basu yadda da cewa Abdul din yayi aure ba da gaske, saida ya fito a wani faifan Bidiyo yana gayawa mutane cewa hotunan da aka gani da gaskene.

Wata ma’abociyar shafukan sada zumunta, Meenah M. Sadeeq da take mayar da martani kan wannan lamari ta bayyana cewa babu wani abin abi dan mace me shekaru 40 zuwa sama ta auri matashi dan kimanin shekaru 30.

Ta kara da cewa, idan dai Tsoho ,zai auri budurwa me shekaru sha ko ashirin da wani abu to suma mata zasu iyayi.

Ta yi kira ga mata da suka manyanta dasu dain jira wai sai mai kudi zasu aura, tace ki tashi ki nemi kudin kema sai ki auri matashi irin wanda kikeso.

Ga cikakken bayanin nata kamar yanda ta saka a shafinta na sada zumunta.

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2921614521267764&id=100002577345235

Tace itama nan bada dadewaba za’a ganta da rangadeden Saurayi.

2 Comments

Back to top button
error: Content is protected !!