Nigeria Ta Karyata Sanya Hannu A Yarjejeniyar Da Za Ta Tallafawa ‘Yan M*digo Da Lu₩adi
Nigeria Ta Karyata Sanya Hannu A Yarjejeniyar Da Za Ta Tallafawa ‘Yan M*digo Da Lu₩adi
Gwamnatin Najeriya ta karyata batun rattaba hannu kan yarjejeniyar kasashen Afurka da Caribbean da Pacific da kasashen Turai don neman bashi.
Ministan kasafi da tsara tattalin arziki Sanata Atiku Bagudu ya bayyana haka lokacin da yake jawabi don fayyace rahoto da ake bayarwa cewa Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar ta Samoa don neman bashin Dala miliyan 150 daga Kungiyar Tarayyar Turai EU.
A yayin jawabin nasa a wajen taron da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a ya shirya a Abuja yace ba gaskiya bane cewa Najeriya ta sanya hannu a yarjejeniya da ke nuna goyon baya ga ‘Yan Lu₩adi Da M@digo LGBC.
Ministan ya jaddada cewa abin da za a amince, sai ya bayyana a fili za a kare bukatun kasashen Afurka a wasu fannoni bayyanannu.
Sanata Bagudu yace bangarori da Najeriya za ta nemi hadin kai kansu sun hadar da dorewar ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya da tsaro da sauyin yanayi da kare hakkin bil Adama da dimukuradiyya da shugabanci.
Ministan ya ba wa ‘yan Najeriya tabbaci cewa gwamnati ba za ta sa hannu ba a kowace yarjejeniya ba da za ta zama kalubale ga addini da al’ada da kimar al’ummar Najeriya.
Yace babu wani bangare da ya zama barazana ga kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar kasar da yin tuntuba da ta dace kafin sanya hannu a yarjejeniyar ta Samoa.
Ya shawarci ‘yan Najeriya da su tallafa wa kokari da shugaban Najeriya Tinubu ke yi wajen jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen na Kungiyar Tarayyar Turai.
Ministan yada labaran da wayar da kan jama’a Alhaji Muhammed Idris yace gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta taba sa hannu a wani abu ba da zai cutar da muradun ‘yan Najeriyar ba.
Yace gwamnatin Najeriya ba ta ji dadi ba kan yadda ake ba da bayanai wadanda ba na gaskiya ba kan yarjejeniyar ta Samoa
Ministan ya kara da cewa an nemi malamai da sauran masu ruwa da tsaki kan sha’anin don tabbatar da nasarar tsare-tsaren gwamnati ta yadda za a samu jan hankalin masu son zuba jari a kasar.
Source: VON Hausa