Ni Ba Shegiya Bace, Da Ubana, Murtanin Umma Shehu Kan Adam A Zango
Wani sabon rikici ya barke tsakanin fitaccen jarumi Adam A Zango da kuma jaruma Umma Shehu
Wani sabon rikici ya barke tsakanin fitaccen jarumi Adam A Zango da kuma jaruma Umma Shehu
Rikicin dai ya biyo bayan wani zagi da jarumi Adam Zango yayi a lokacin da yaje wani wasa a jihar Kano
Inda yake cewa kowane shege ko shegiya a Kannywood wadannan mutane da suka fito kallon shi sune gatan su
A makon da ya gabata ne jarumi Adam A Zango yayi wani furuci a lokacin da yaje wajen wani taro na masoyansa a jihar Kano, inda yake cewa; “Ko wane shege da shegiya a masana’antar mu kune gatansa.”
Wannan furuci da jarumin yayi ya harzuka mutane da dama a masana’antar inda mutane ke ganin cewa jarumin bai kamata ya furta wannan kalmomi ba, har wasu mutane ke tunanin cewa kodan saboda ya bar masana’antar ne yasa yayi wannan furuci?
Sai dai jaruma Umma Shehu ta kasa jure wannan kalamai na jarumin, inda ta fito ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram ta ke cewa:
“Kowanne shege da shegiya kune gatansa, amma ina so ka sani Annabi ne ya fada yace kyakkyawar kalma sadaka ce, ina so Adam A Zango ya sani cewa ni ba shegiya bace da ubana kuma ‘yar sunnah ce ni dan haka ka cireni a cikin shegun.
“Duk ‘ya ta halak tana kishin iyayenta, idan baki ya san abinda zai fada bai san me za’a mayar mayar masa ba, tunda kace kowa yana nufin harda wadanda suka zo yau kenan dan haka ka cireni daga cikin shegun dab ni ba ita bace ka gane?
“Shi zagi ko wulakanci sai ka bada dama wani ma yake samun daman yi maka, duk abinda mutum zai yi sai ya sayawa kansa mutunci kafin wani ya girmama ka. Dukan mu muna aibata kan mu, to daga yaya wasu wadanda basa cikin mu za su mutuntamu.
“Ka fadi alkhairi ko kayi shiru, yadda zaka yi wannan zagin a cikin mutane ai ka basu dama kenan, gaskiya wannan ba daidai bane sai ka mutuntamu sannan wasu za su gani su mutuntamu wannan shine.”