Kannywood

Ni Ba Mahaifiyar Ummi Rahab Bace – Inji Matar Da Akace Itace Mahaifiyarta

An Yanka Ta Tashi, Matar Da Akace Itace Mahaifiyar Ummi Rahab, Ta Fito Ta Karyata Batun Inda Tace Ita Ba Mahaifiyarta Bace,

Yayin da kwana biyu batun rikici tsakanin jaruma Ummi Rahab da fitaccen jarumi Adam A Zango ya yi sanyi, wanda a baya lamarin ya tada kura matuka da har ta kai ga an fara bincike dangane da ainahin iyayen jarumar.

Wani da ya bayyana kanshi a matsayin marikin jarumar, mai suna Yasir M. Ahmed ya wallafa wasu hotuna guda biyu a shafinsa na Instagram inda yake nuni da mahaifiyar jarumar da kuma mahaifinta, wanda ya bayyana cewa duka mazauna kasar Saudiyya ne.

To sai dai kuma kwatsam wani bidiyo da ya fito yake yawo a cikin wannan makon ya nuna wata mata da ta fito take ikirarin cewa ba ita ce mahaifiyar jarumar ba, hasalima ba ta da wata alaka ko ta kusa ko ta nesa da jarumar.

Ga dai abinda matar ta ce bayan wata mai suna fardous00 ta yi mata tambayar cewa ko ita ce Babar Ummi Rahab, sai ta ce:

To Firdausi zan baki amsar ki, da kika ce ko kece babar Ummi Rahab, ni ba Babar Ummi Rahab bace, ban taba ganinta ido da ido ba, amma ‘yar uwata ce a Musulunci, shine kawai iya abinda na sani. Mutane da dama suna tambayata ina da alaka da ita, bani da alaka da ita gaskiya.

Haka ita ma wata mai suna yarmama25 ta sake cewa ta ga an sanya hotonta da wani balarabe akan cewa sune iyayenta, sai ta ce:

Na gaji da amsa wannan tambayar, na riga da tun farko na bayyana cewa bani da alaka da ita, ban kuma san Ummi Rahab ba sai dai kawai alaka ta Musulunci, tiktok ku shaida na yi ‘ya daga yau nima na huta da amsa wannan tambayar.

Sai dai da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta tuntubi Yasir kan wannan bidiyo, ya bayyana mata cewa matar dai taga hoton yayi kama da nata ne, amma ba ita ba ce ta jikin hoton da ya nuna ba.

Mahaifiyar Ummi tana nan wannan kuma wal’Allah gani tayi suna kama da hoton da ya yada shi yasa ta fito tana wannan magana, amma wadannan hotuna da ya yada tabbas sune iyayen Ummi Rahab.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Mun Samo Muku Wannan Labarin Daga Shafin LabaranHausa.Com

Back to top button
error: Content is protected !!