Nayi mamakin baiwa Fati Washa Gwarzuwar Kannywood –Kamaye
Fitaccen marubucinnan kuma jarumain fina-finan Hausa Dan’azimi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa wanda akafi sani da Kamaye ya bayyana cewa yayi mamaki matuka ganin yadda aka zabi jaruma Fati Washa matsayin jarumar Kannywood,dalafim na ruwaito.
Cikin wata tattaunawa da Kamaye yayi da Dala FM ya bayyana cewa jaruma Jamila Nagudu ce tafi can-canta da zamowa tauraruwar Kannywood saboda la’akari da kwarewarta a harkar Film, kuma ita ce tauraruwar jarumarsa a masana’antar.
Kamaye ya kara da cewa ita Jamila Nagudu babu wani abu da zaka sanyata tayi maka shi a Film da ba zata iya yi ba, a don haka yayi mamaki matuka da masu zabar tauraruwar basu zabi Jamilan ba.
Idan zaku iya tunawa dai a watan Nuwamban da ya gabata ne jaruma Fati washa ta lashe kyautar gwarzuwar fina-finan Hausa, a yayin wani taron fina-finan Africa da aka gabatar a birtaniya.