Kannywood

Na koma “Nationalwood” daga “Kannywood” –Inji Naburaska

Jarumin wasan kwaikwayonnan kuma jarumin barkwanci Sharu Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Naburaska ya bayyana cewa ya koma masana’antar shirya fina-finai ta kasa wadda ya kira da “Nationalwood” biyo bayan ficewarsa daga masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Naburaska ya bayyana cewa ya fice daga masana’antar Kannywood sakamakon abubuwa na rashin adalci da yaga ana gudanarwa ciki har da yadda aka cafke wasu abokanan aikinsa ba bisa ka’ida ba.

Yayin da yake zantawa da Freedom Radio a safiyar yau Litinin ya bayyana cewa a yanzu haka tuni ya gama cika dukkan sharudan da suka kamata tsakaninsa da hukumomi na kasa, wanda suka sahale masa gudanar da al’amuransa.

Back to top button
error: Content is protected !!