Na Fita Daga KannyWood – Adam a zango

Shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana cewa ya fice daga masana’antar.
Adam Zango ya bayyana cewa ya bar Kannywood daga ranar yau Alhamis, 15 ga watan Agusta, inda ya bayyana cewa daga yanzu duk wani abu da zai yi baya bukatar a danganta shi da masana’antar.
Ya kuma jadadda cewa duk wani arziki ko rashinta a Kannywood baya bukata, ya ce zai fara cin gashin kansa.
Jarumin ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin shugabancin kama karya da ake yi, mai karfi, mai daukaka, mai arziki, mai daukaka ba a iya hukunta shi saboda kwadayi da son zuciya.
Ga yadda jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram:
A baya mun ji cewa Adam A. Zango ya yi martani akan kamun jarumi Sanusi Oscar da jami’an tsaro suka yi a jihar Kano.
Adam Zango ya bayyana cewa a yanzu Sanusi ya sake samun sabuwar ilimi, inda ya karfafa masa gwiwa akan cewa komai mai wucewa ne.
Har ila yau Zango ya bayyana cewa kamar yadda yake bayar da labarin shiga gidan yari a yanzu, wata rana shima Oscar zai bayar don haka yayi hakuri.