Na Daina Yin Fim Din Hausa – Jaruma Radeeya Jibril
Jarumar KannyWood Radeeya Jibril Ta Bayyana Cewa Ta Daina Yin Fim Sakamakon Auren Sirri Da Tayi.
Jarumar Ta Bayyana Hakan Ne A Shafinta Na Instagram, Inta Tayi Godiya Sosai Ga Dukannin Jaruman KannyWood Da Abokan Aikinta Da Masu Shirya Fina Finai Na Masana’antar KannyWood. Inda Tayi Godiya Ga Masoyanta Na Fadin Duniya.
Assalamu alaikum barka da safiya yan uwa
da masoyana ina yina kowa fatan alkairi sannan ina taya murnar shiga sabuwar shekara SUNANA RADEEYA JIBRIL kamar yanda kuka sani Sannan kuma ni matashiyar jaramur kannywood ce kamar yinda kuka sani to Alhamdulillah ina alfahari da kasance wata yar film Sannan kuma zanyi anfani da wannan damar tawa tayau domin sanar daku cewa (NAYI AURE) Nagode wa Allah daya nunamin wannan rana ranar dazan bar kannywood lfy kamar yinda nashigo lfy Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah.
Dan Allah duk wanda naiwa ba daidai ba ya yafemun Ni daman ba wanda yamun.
SUNCLE Ty Shaba @official_tyshaban bansan da wace kalma zan gode masa ba domin kuwa ya taka babbar rawar gani acikin rayuwa tah a kannywood wanda yaza memun bango jigo gwarzo YAYA
Ina alfahari dakai uncle Allah ubangiji yasaka maka da mafificin alkairi Allah ubangiji kaima ya duba bayanka ko bayan ranka Allah ubangiji yasaka maka da gidan aljannah Findausi Nagode @official_tyshaban.
Sannan zanyi anfani da wannan damar wajen godewa @realabmaishadda Ya daukeni tamkar kanwar sa yabani gudun mawa yana farin ciki da duk wani abun alkairi dazai sameni sai dai nace Allah ubangiji yasaka masa da alkairi Allah ya kara daukaka darajar ka
Sannan ina mika godiya ta ga @reelumaruk wanda ya daukeni tamkar kanwar sa yabani gudun mawa mai tarin yawa da shawarwari wanda zasu anfaneni sai dai kawai nace Allah ubangiji yasaka masa da mafificin alkairi A
Sannan ina mika godiya wa @abdulamart_mai_kwashewa
wanda ya rike hannuna da niyyar yimun abubuwan alkairi na cigaban rayuwata gsky babu abunda zance saidai nace
Allah ubangiji yasaka maka da mafificin alkairi Allah ubangiji yakara haskaka maka al’amuran A _A A,
Sannan Ina mika godiya wa @ahmadbifa007 wanda Allah ya hadamu a lokaci daya ya daukeni tamkar yar uwarsa nagode yaya Ahmad Bifa mutun mai hakuri mutumin kirki
@real_mujahid_m.soja kai na daban ne 1Allah ubangiji yaci gaba da daga darajar ka 10
Ina yiwa alummar kannywood godiya tare da fatan alkairi Allah ubangiji ya biyawa kowa bukatun sa na alkairi.