Na Amince Da’na Ya Bi Ki, Inji Mahaifiyar Wanda Wata Baturiya Ta Biyo Shi Har Kano Daga Amurka
Fatima Suleman Mahaifiyar matashi Suleman ta amince dan ta mai shekaru 23 ya bi masoyiyarsa mai shekaru 45 wacce tsuntsun soyayya ya dauko ta daga Amurka domin haduwa da masoyin ta da suka hadu a kafar sadarwa ta Instagram.
Baturiyar Birnin Carlifonia ta zo daga Amurka har unguwar Panshekara dake Kano domin tabbatar da soyayyar ta ga matashi Suleman wanda suka dade suna tsinkar fure a shafin sadarwa.
Yanzu haka da zarar an kammala shirye-shirye za ta saka masoyin ta a gaba su wuce Amurka.
Fatima Suleman mahaifiyar matashin kuwa ta ce ba ta da suka don haka ta amince da soyayyar.
Shi ma ango Suleman ya ce dama burinsa shine ya haifi ‘ya’ ya ruwa biyu barbarar yanyawa (half cast) gashi kuma ya tsinci dami a kala.
Ya kuma alkawarin zai dinga kawo ziyara ana gaisawa.