Labarai

Muyi Korafi Kuma Muyi Hakuri Ga Shugaba Tinubu

MU YI KORAFI MU KUMA YI HAKURI – SAKON HADIMA GA SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU SAYYADA RAHMA ABDULMAJID

A gaskiya ana jin jiki daga sama har kasa, tashin dala, tashin abin masarufi, karancin kudi, karuwar talauci da yunwa. Ga kuma matsalolin tsaro, dole yan kasa mu yi fushi, mu kuma harzuka, Yunwa da rashin tsaro abin tayar da hankula ne, babu me ganin laifin wanda hankalinsa ya tashi saboda hakan. Don haka wallahi ba ma ganin bekenku, hasali ma har yau ban taba shiga wani dakin taro a Villa na ji ana zargin talaka don yayi fushi ba.
Sai dai ga shawarwari

1 KU YI KORAFI: Korafi wani lokaci tamkar shawara ne ga mahukunta, tare da bayyana yanayin da mutum ya sami kansa, kuma yana rage radadi, Mu ma mun yi a baya don haka dole a mana, yana matukar taimakonmu fiye da cutar da mu

2 KU YI HAKURI:
Sai dai yaya za a yi? Dole mu baku hakuri, ku yi hakuri, Mu yi hakuri. Wallahi wallahi ana aiki babu dare babu rana, da ace ba a aikin wallahi da ba zamu zauna a wurin ba ma, Don ko da baku yarda mun damu da ku ba, ku yarda da cewa mun san zamu gamu da Allah kuma muna tsoron hakan. Yanayin da Najeriya ta sami kanta sakamakon sakacin da aka yi a baya dole sai an sha radadi a yayin daukar wasu matakai da sauye-sauyen da zasu iya kai ta ga farfadowa. Kuma a iya sanina da su shugaban kasa da mataimakinsa ke kwana su tashi

3 KU YI WATSI DA JITA-JITA.
Ku bibiyi kafofin labarai na gaske maimakon na masu sharhi. Babu wani shiri na sauya birnin tarayya da ke gudana a yanzu a iya sanin mu, lalacewar mu bata kai ta a hada baki da mu a cutar da jama’a ba. Bari na muku wani fashin baki, Legas din kanta bata bukatar zama birnin tarayya a yanzu tunda ta gano irin ci gaban da zata iya samu zai iya dorewa ne idan bata matsayin tarayyar kasa wanda kan mai da wuri na kowa da kowa. Jahar Legas na gasar zama babban birnin kasuwancin Africa ne ba na tarayyar Najeriya ba, wannan ne tunanin ‘ya’yanta. Su kuwa ma’aikatun da aka mayar can Ku bibiyi dalilai da tarihin yin hakan Ko ku bibiyi shafin mu na @Sabuwar Nigeria don samin labarin hakan.

4 KYAKKYAWAN FATA:
Kwarai ana jin jiki amma mu yi hakuri za a farfado, Muna muku Albishir da aiyukan da muka ga ana yi kuma an taso su a gaba babu dare babu rana inshaAllah zamu more su nan kusa, Naira zata farfado, aiyukan yi zasu samu, Tattalin arzikin Najeriya zai sake yin karfi, babu yajin karatu ba, babu na maaikata, za a kara albashi, Wallahi wallahi ban san wani ba, amma ni dai Rahma wannan ne ke rike da ni a gwamnati ba albashi ko alawus ko wata dama ba, na ga ana aikin farfado da kasa ne na ke so ni ma na sami ladar hakan. Wallahi ko yau na fahimci sabanin hakan tabbas, to ni mai hakura da aikina ce na koma gwagwarmaya. Ban fadi wannan don ku yarda ba sai don Allah Ya shaida.

Daga Rahama Abdulmajid (Hadimar Shugaban Najeriya Bola Tinubu fannin sadarwa)

A YI HAKURI!!!
AQUULU QAULI HAZAA, ASTAGHFIRULLAHA LI WA LAKUM

Back to top button
error: Content is protected !!