Kannywood

Mutum Hudun Nan Sun Isa Yan KannyWood Wa’azi

Iya Mutum Hudunnan Kawai Sun Isa Jaruman Masana’antar KannyWood Wa’azi Kuma Za.a Gane Maganar Da SarKin Waka Yayi Akansu Akwai Kamshin GasKia.

Wadannan Jaruman Guda Hudu A Baya Kowannen Su Yaci Zamaninsa Daga Baya Kuma Su Hadu Da Kaddarar Rayuwa, Nan Kuna Kowa Ya Nuna Ba Ruwansa Akai.

Sani Moda, Malam Waragis, Sani SK, Duk Sunsha Fama Da Doguwar Jinya. Inda Daga Baya Malam Waraagis Allah  Ya Masa Cikawa, Sani SK Ma Allah Ya Karbi Rayuwarsa.

Shi Kuma Sani Moda An Yanke Mishi Kafa Ne Sabida Fama Da Yayi Da Ciwon Suga, Bashir Ciroki Shi Kuma Fama Yayi Da Halin Rayuwa Inda Aka Daina Sashi Cikin Fina Finai.

Kuma Ya Dawo Bashi Da Wata Sana’ar Daya Dogara Da Ita. Nan Ne Dai Mutane Ke Ganin Cewa Kamar Masana’antar KannyWood Basu Da Tsari Kuma Basa Iya Taimakawa Tsofaffin Jarumansu. Musanman Wanda Su Hadu Da Iftila’in Rayuwa.

Cikin Kwanakin Nan Ne Dai Tsohuwar Jaruma Ladin Cima Wacce Akafi Sani Da Baba Tambaya Ta Bankado Wani Sirri Da Ba Kowa Ya Sani Ba.

Inda Ta Bayyana Cewa Ita Idan Ansata A Fim. Kwata Kwata Bai Wuce A Bata Naira Dubu Biyu Ko Dubu Kudi, Inda Wannan Maganar Ya Tayar Da Qura. Aka Dinga Fitowa Ana Karyata Maganar Musanman Ma Masu Shirya Fina Finai.

Idan Hakane, Zamu Iya Cewa Kenan Yawancin Jarumai Mata Musanman Matasan Yan Mata Da Suke Shigowa Lokaci Daya Suyi Suna Kuma Su Sami Kudi Ba Harkar Fim Din Ke Basu Kudinan Da Muke Ganin Suna Fantamawa Ba.

Back to top button
error: Content is protected !!