Mutane Da Yawa Sun Gyaru Saboda Mu, -Teema Makamashi
Sananniyar jarumar masana’antar Kannywood din nan da ake kira da Teema Makamashi, ta karyatar cece-kucen jama’a da suke cewa jaruman masana’antar Kannywood din basu da tarbiya.
Yayin tattaunawa da jarumar ta yi da gidan rediyon Freedom da ka Kano, ta bayyana cewa “Mu muke da tarbiya kuwa saboda mu ke bada gudummawa wajen gina tarbiyar ‘ya’yan mutane. Nasan wadanda suke yawace-yawacen sata, karuwanci da sauran munanan lamurra amma sanadiyyar wani fim da suka kalla, duk sun daina”.
Jarumar ta kara da cewa, mafi yawan bakin haure a masana’antar Kannywood din ne ke bata musu suna, amma su ‘yan fim mutane ne masu daraja da tarbiyya.
Sanannen abu ne dai yadda iyaye da masu ruwa da tsaki a al’umma ke Alla-wadai da wasu al’amuran na masana’antar Kannywoood din.
A kan danganta tabarbarewar tarbiyya a kasar hausa, ballantana arewacin Najeriya da irin rawar da ‘yan fim din ke takawa. Sau da yawa matasa na kallon ‘yan fim din ne a matsayin madubin dubawarsu ta bangarorin rayuwa da dama.
Sai dai kash! Wasu daga cikinsu kan bayyana alfasharsu kiri-kiri a duniya. Ta yadda suke saka sutura, ma’amala da mutane da sauransu, duk babu abun birgewa.
A wani bangaren kuwa, saboda ba duka ne aka taru aka zamo daya ba, a kan samu wasu masu kyakyawar tarbiya da dabi’a a cikinsu.