Kannywood

Maryam Wazeery Ta Amarce

Jaruma Maryam Wazeery Wacce Akafi Sani Da Laila A Cikin Shirin LABARINA Ta Amarce A Ranar Jumma’a 26/11/2021, Inda Jarumar Tayi Auren Bazata, Ba Wanda Ya Sani Sai Lokaci Guda.

An Sami Sanarwar Auren Nata Ne Bayan Da Shugaban Kamfanin Saira Movies Yayi Sanarwa A Shafinsa Na Sada Zumunta Inda Yayi Sanarwa Kamar Haka

A madadina da Kamfanin @sairamoviestv Muna taya β€œYar uwa @maryamwazeery Murnar Auren da tayi a yau. Allah ya basu zaman Lafiya, Allah kuma ya basu zuriya dayyiba πŸ™ congratulations πŸΎπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽˆ muna missing din ki LAILA πŸ™Œ #LABARINA

Ba Yau Jaruman KannyWood Su Fara Irin Wannan Auren Ba Na Lokaci Daya. Ko A Baya Bayan Nan Jaruma Zahra Diamond Itama Tayi Irin Wannan Auren Na Lokaci Guda. Sai Kuma Rahama MK. Wacce Akafi Sani Da Hajiya Rabi Bawa Mai Kada Itama Ta Amarce Na Sirri.

Muma Muna Fatan Allah Ya Bata Zanan Lafiya Ya Kuma Albarkace Auren Nata Da Tayi. Amin

Back to top button
error: Content is protected !!