Labarai

Zazzafar Martani Ga Dauda Rarara Kahutu

Zazzafar Martani Ga Dauda Rarara Kahutu Kan Bidiyon Hirar Da Yayi Inda Ya Kalubalanci Mulkin Buhari, – Daga Bashir Ahmad

Dauda Rarara Kahutu

Na kalli wani bangare na videon da yake yawo na taron manema labarai da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gabatar a yau, musamman bangarorin da ya ci wa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari mutunci tare da zargin cewa sai da ya rusa kasar baki daya kafin ya bar mulki.

Bayan kammala kallon video na yi yunkurin bawa Rarara amsa daya bayan daya ga duk wadannan zarge – zargen da yayi, sai dai daga bisani da na sake yin nazari a tsanake sai na ga babu bukatar hakan a halkance da kuma mutunce, saboda wasu dalilai kwarara guda biyu.

Na farko, cikin videon, Rarara yayi ikirarin cewa wai gudunmawar daya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai bawa kan sa irin wannnan gudunmawa ba. IKON ALLAH. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana?

Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a bashi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a bawa mukaman na ministoci. TASHIN HANKALI. Ko akwai chemistry, balle technology a cikin wannan batu?

To gaskiya wanda maganganu da suka fita daga bakin mawakin ya sa na ga cewa tsayawa a bashi amsa a matakin hankali ma bata lokaci ne, domin kuwa wadannan maganganun na sa sun saba da kowane irin hankali da tunani, idan dai ba akwai rashin lafiya ba, to lalle akwai tsantsar jahilci. Babu hikima a cikin maganganun nasa ko kadan.

A kuma maganar da Rararan yayi da cewa wai a cikin shekaru bakwai na Baba Buhari ba a iya bin hanyar Abuja zuwa Kaduna, a zahirin gaskiya ba zan ce ba a samu matsalolin tsaro a hanyar ba, sai dai zan dan yi masa tuni da ya tuna baya a lokacin da Baba Buharin ya karbi mulki, ba ma maganar kidnapping ake yi a hanyar ba, Saboda matsalar da Boko Haram ta jefa yankin Arewa daga Abuja zuwa Kaduna sai an ci karo da shingen jami’an tsaro sama da goma, ba ma maganar daga Kaduna zuwa Kano ba, balle uwa uba, daga Kano zuwa Maiduguri. Duk wanda yake da hankali zai godewa Allah akan wannan.

Game da wakokin da yayi wa Baba Buhari, tunda Rarara yake yi masa waka, bai taba yi masa waka kyauta ba tare da an biya shi hakkin sa ba.

A karshen magana daya da Rarara ya manta bai fada ba ita ce bai fito ya bayyanawa jama’a cewa Baba Buhari bai taba taimakon sa a rayuwarsa ba.

Back to top button
error: Content is protected !!