Kannywood

Muna yin Fina finan Hausa ne dai-dai da addini Musulunci -Inji Furodusa

Fitaccen mai shirya fina finan Hausa nan Sani Ali Abubakar Indomie ya bayyana cewa fina-finan da sukeyi suna yinsu ne dai-dai da addinin Musulunci.

Sani Indomie ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan sabon film din da ya shirya na “Karamin Sani” inda yace kacokan wannan shiri ya mayar da hankali ne kan koyar da al’umma kaidata ubangiji madaukakin sarki wato Tauhidi.

“Acikin fina-finai na babu rawa kuma babu kida, saboda ya dace da tsari irin na addinin Musulunci” a cewar Sani Indomie.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da wasu al’umma ke kallon masu shirya fina-finan Hausar na wuce makadi da rawa wajen tsikarar al’ada da addinin malam bahaushe.

Back to top button
error: Content is protected !!