Kannywood

Muna da alaka mai kyau da ‘Yan sanda -Rukayya Dawaiya

Fitacciyar jarumar nan Rukkaya Umar da aka fi sani da Rukayya Dawaiya ta bayyana cewa suna da kyakkyawar alaka da hukumomin ‘Yan sanda domin suna matukar taimaka musu wajan gudanar da wasannin kwaikwayo.

Rukayya Dawayya ta bayyana haka ne lokacin da take tattaunawa ta musamman da Freedom Radio.

Tace hukumar ‘Yansanda tana basu kayan sawa,da motocin da suke jerin gwano da kuma basu Dansandan da zai ke nuna musu yadda ake sa kaya da maganganu da ‘’Yansanda.

Yar wasa Rukayya Dawaiya tace inda har sun turawa hukumar ‘Yan sanda da takardar sanarwa da kuma abin da suke bukata kafin lokacin gudanar da wasan su basa samun matsala.

Ta kara da cewa ta shafe tsawon kamar shekara sha biyar ta na sana’ar wasan Hausa,inda tace ta samu nasarori da yawa a sana’ar.

“Daga cikin nasarorin da nake alfahari da shi akwai alfaharin da mijina ke yi da ni na samun fitacciyyar jaruma wacce al’ummar Duniya ke alfahari da ita”
Tace matsalolin da suke samu a da na guraran da za su gudanar da wasa ya zamo tarihi tun da a yanzu suna samun gidajen mutane da na ‘’Yan kasuwa da gidansarauta da gidajen Malamai.

FREEDOM RADIO

Back to top button
error: Content is protected !!