Labarai

Muna Allah Wadai Da Tura Dalibai Kasar Waje Da Gwamnatin NNPP Ta Yi

Muna Allah Wadai Da Tura Dalibai Kasar Waje Da Gwamnatin NNPP Ta Yi A Kano Domin Ba Wannan Ne Bukatar Kanawa Ba A Yanzu, Cewar Jam’iyyar APC

Babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano, ta soki tsarin tura dalibai karatu zuwa ƙasashen ƙetare domin yin karatun digiri na biyu a fannonin ilimi daban daban, inda tace daɓen kwalo ne kawai, domin babu bukatar hakan a halin yanzu.

Kakakin jam’iyyar, Ahmad S. Aruwa ne ya bayyana haka, inda yace anfi bukatar a inganta ilimin cikin Gida kafin a tafi ƙasashen ƙetare, saboda haka basu gamsu da wannan tsari ba, domin daga baya ma za’a iya jiyo koke-koken daliban akan batun kuɗin makaranta.

A ranar Juma’a ne dai rukunin farko na daliban da suka fita da sakamakon mafi kyau a karatun digirin farko yan asalin jihar Kano, suka tashi zuwa ƙasar India domin karatun digiri na biyu, wadanda gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta dauki nauyin su.

Daga Jaridar Dokin Karfe

Back to top button
error: Content is protected !!