Kannywood

Mu mukayi sakaci Kannywood ta lalace –Kamaye

Jarumin fina-finan hausar nan Dan’azimi Baba wanda akafi sani da Kamaye ya bayyana cewa sune sukayi sakaci masana’antar shirya fina-finan hausa ta lalace.Kamaye ya bayyana hakan ne ya yin wata zantawa da yayi da Freedom Radio inda ya ce su ne suka tsugunna suka haifi masana’antar Kannywood amma saboda rashin kulawa ta musamman da daukarta da muhimmanci da basuyi ba a baya, ya haifar da koma baya a masana’antar.Jarumi Kamaye ya kara da cewa a baya ba suyi tsammanin masana’antar zata kai haka ba, shi ne abinda ya sanya basu bata muhimmancin da ya kamata ba, amma yanzu cikin ikon Allah masana’antar ta wuce yadda ake tsammani.

Back to top button
error: Content is protected !!