E News

Ministan Noma Wajen Saffara Tumatur a Kebbi

Ministan Noma Ya Wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed TINUBU Ya Bude Wajen Sarrafa Tumatur Na (GB FOODS) A Jihar KEBBI

Mai girma ministan noma na ƙasa, Sen. Abubakar Kyari CON, ya wakilci mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buɗe masana’antar sarrafa tumatur a Ngaski, Jihar Kebbi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Girman masana’antar ya kai adadin hecka 1500 wadda a kullum za a iya sarrafa metrik ton 620, sannan kuma za ta iya samar wa mutum 5,000 aiki wanda mata za su ja kaso 70 daga ciki. Ta kasance babbar masana’antar sarrafa tumatur a Afrika.

Wannan cigaba ya dace da ƙudirin mai girma shugaban ƙasa Tinubu na ƙarfafawa masu zuba jari gwiwa su zuba jarinsu a harkar noma domin samar da ƙarin guraben ayyukan yi cikin manufofinsa takwas.

An fara aikin tun zamanin Sanata Atiku Bagudu yana matsayin gwamnan Jihar inda gwamna mai ci a yanzu Dakta Nasir Idris ya kammala. Taron ya samu halartar ministan yaɗa labarai Muhammad Idris wanda shi ma ya yaba da aikin.

Minista Kyari, ya jinjinawa kamfanin samar da abinci na (GB FOODS) tare da godewa Jakadan Spain Juan Sell bisa babbar rawar da ya taka wajen ƙulla wannan alaƙa tsakanin Najeriya da ƙasar ta Spain.

Back to top button
error: Content is protected !!