Labarai

Mijina GFresh Al-Amin Ya Sakeni Tun A Watan August

Mijina GFresh Al-Amin Ya Sakeni Tun A Watan August – Cewar Sayyada Sadiya Haruna

A Wani rahoto da jaridar Dokin Karfe TV ta samu, Sayyada Sadiya Haruna ta bayyana cewa halin da ake ciki yanzu babu aure a tsakaninta da angonta, Al’ameen G-Fresh saboda ya sake ta tuntuni. “Ya sake ni tun a watan Ogas”. Ta ce.


Sadiya Haruna ta kuma ƙara da cewa G-Fresh ya buƙaci ta biya shi dukkan kuɗaɗensa da ya kashe wajen hidimar aurenta kuma ta ba shi.


Sai dai kuma, a nasa ɓangaren, Al-Ameen ya bayyana cewa atafau fa shi bai saki matarsa ba, akwai aure a tsakaninsu wani ne dai da ke zaman P.A ɗinta ya ke hure mata kunne domin har abinci su ke ci tare shi kuma a matsayinsa na mijinta ta zuba mas a wani kwanon daban.


“Ko da wasa ban saki matata Sadiya Haruna ba auren soyayya mu ka yi”. Cewar G-Freesh ɗin.

 

Back to top button