Kannywood

Meyasa Nafeesat Abdullahi Ta Daina Fitowa A Fina Finan Hausa

Shahararriyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta shilla kasar Ingila domin yin karatu na musamman a fannin daukar hoto da sauran harkokin da suka shafi bada umarni a finafinai.

Jarumar wadda ta yi shahara matuka da gaske, ta shaida mana cewar za ta yi wannan karatu ne domin kara samun kwarewa da gogewa a fannin harkokin finafinai, musamman da a yanzu take sa ran fara bada umarni a finafinan kamfaninta.

A kwanakin baya dai Nafisa Abdullahi ta bayyana aniyarta na fara daukar nauyi da kuma bada umarni karkashin kamfaninta, wanda ya sa masana ke ganin lallai wannan karatu da za ta yi zai yi mata amfani matuka da gaske.

Northflix ta samu labarin,Tun ma kafin ta tafi kasar Ingila wannan karatu, Nafisa ta kai ziyarar musamman kasar Amurka, inda aka gan ta tsamo-tsamo cikin masana’antar Hollywood rike da kyamara tana zagayawa. Har ila yau, an gan ta manyan wuraren shirya finafinai a kasar Amurkan.

Sai dai, wannan tafiya ta Nafisa ta zo a daidai lokacin da Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano ke aikin tantance masu sana’ar fim, musamman da yake Kanon ita ce ake yi wa kallon cibiyar Kannywood, lamarin da wasu ke ganin kamar hakan da ta yi ya nuna ba ta damu da harkar tantancewar ba.

Mun yi kokarin jin ta bakinta kan wannan lamari, amma abun ya ci tura, kasancewar tuni jarumar ta mayar da hankali wajen yi wannan karatu a Babbar Makarantar Koyon Daukar Hoto da ke Birnin Landan, a kasar Ingila.

Daga Nothflix

Back to top button
error: Content is protected !!