Labarai

Mesut Ozil ya soki China kan gallaza wa Musulmi

Dan wasan tsakiyar Arsenal Mesut Ozil ya soki kasar China kan yadda take muzguna wa Musulmi ‘yan kabilar Uighur na yankin Xinjiang.

Ozil wanda Musulmi ne, ya siffanta Musulman kabilar ta Uighur da cewa “jarumai ne masu yaki da zalunci” a shafinsa na sada zumunta.

Sannan kuma ya soki sauran kasashen Musulmi bisa shurun da suka yi.

Sai dai mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Geng Shuang, ya ce “an rudi Ozil ne da labaran kanzon kurege” kafin ya yi maganar.

Geng ya ce: “Ban sani ba ko Ozil ya taba zuwa Xinjiang da kansa, amma da alama an rude shi ne da labaran kanzon kurege sannan kuma abin da yake fada yana cike da karairayi.

“Idan Ozil ya samu dama, za mu so ya ziyarci Xinjiang domin gane wa idonsa.”

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama sun bayyana cewa kusan miliyan daya ne – akasarinsu Musulmai ‘yan kabilar Uighur – aka tsare a gidajen yari masu tsattsauran tsaro, ba tare da shari’a ba.

China ta sha musanta zargin muzguna masu, inda ta ce ana “ilmantar da su ne a cibiyoyin gyara hali” domin kakkabe tsattsauran ra’ayin daga zukatansu.

Jim kadan bayan kalaman na Ozil, gidan talabijin na CCTV, mallakar gwamnatin China, ya cire wasan Premier tsakanin Arsenal da Manchester City daga jadawalin wasannin da zai nuna.

Mamallakin shafin bincike na Baidu ya sauke wani zaure na magoya bayan Ozil daga shafinsa sannan ya ce: “Idan ana maganar bukatun kasa babu ruwanmu da abin da wani yake so.”
Hukumar kwallon kafar China ta ce kalaman Ozil “ba abin amincewa ba ne” sannan kuma “sun bata ran” magoya baya.

A ranar Asabar ne Arsenal ta nisanta kanta daga kalaman na Ozil, tana mai cewa “ba ta da bangare a matsayinta na kungiya”.

Ozil ya buga wasan da Manchester City ta doke Arsenal 3-0 a filin wasa na Emirates ranar Lahadi, inda ya nuna bacin ransa a fili bayan an sauya shi a wasan.

Hakan ya jawo magoya bayan Arsenal suka yi masa ihu yayin da yake fita daga filin.

Abin da muka sani game da Musulmin Uighur na China
Uighur kabila ce mai yawan kusan miliyan 11 da ke zaune a yammacin China da ake kira Xinjiang. Mafi yawansu Musulmi ne.

An sha zargin China da tsare ‘yan kabilar ba tare da shari’a ba a gidajen yari masu matukar tsaro, inda ake tilasta masu koyon harshen Mandarin na China, su yi mubaya’a ga Shugaban kasar Xi Jinping sannan a tilasta masu fita daga Musulunci.

China takan ce “ana ilmantar da su ne”, sai dai wasu bayanai da suka bulla wadanda kuma shirin BBC na Panorama ya gani, sun nuna yadda ake azabtar da mutane ta hanyar kulle su da kuma koya masu wani addini na daban.

Sharudan da aka gindaya a cikin bayanai sun hada da cewa a sanya wa cibiyoyin tsauraran tsaro ta yadda ba za su iya guduwa ba sannan a rika bai wa mutane maki gwargwadon “sauyin da suka samu a addinance” da kuma biyayya ga dokoki.

Tsofaffin fursunoni sun shaida wa BBC yadda aka rika azabtar da su a jiki da kuma yadda ake tankwara tunaninsu.

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng
Back to top button